Mi kasani akan WhatsApp TV ???


 WhatsApp TV


1.0 Menene WhatsApp TV


1.1 Abunda Yakamata mu sani dangane da WhatsApp TV 


1.2 Abunda yasa W/ Business yafi


1.3 Abubuwan da ake buƙata dan buɗe WhatsApp TV 


1.4 Yadda za'a samu kuɗi da WhatsApp TV 


1.5. Yadda za'a fara WhatsApp TV


1.6 Rabe-raben hanyoyin samun kuɗi da WhatsApp TV 


1.7 yadda za'a yi growing na WhatsApp TV 


1.8 Kammalawa


Bismillahi rahama-nir-rahim tsira da Amincin Allah subhanahu wata'ala su tabbata ga masoyin mu shugaban mu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama.


Idan ana magana akan WhatsApp TV a ko yaushe mutane kan jin cewa wani application ne daban na WhatsApp TV kokuma wani tsari ne na musamman da su baza su iya ba dalilin kuwa shine an ambaci kalmar "TV"


WhatsApp TV Normal WhatsApp ne da aka tsara shi ta hanyar sanya Videos na nishaɗi da ilmantar wa dama wasu abubuwa muhimmai da ba video ba wannan kuwa ya ƙunshi hotuna, da rubutun zube dss.


Kamar yadda dai muke ganin gidajen Rediyo da TV suna ilmantar wa da nishaɗantarwa bugu da ƙari dakuma jefa neman kuɗin su acikin hakan ta hanyar in streaming, to haka ma WhatsApp TV yake.


1.1. abunda ya kamata mu sani dangane da WhatsApp TV; WhatsApp TV ba wani WhatsApp bane na musamman ko daban a'a WhatsApp de irin na wayata/wayar ku da shi akeyi ƙarƙashin tsarin improvisation wato za'a ƙawata shi yadda za'a gudanar da ayyuka da aikace-aikacen WHATSAPP TV Dan haka abu nafarko shine mun san cewa zamu iya maida WhatsApp ɗinmu ya zama WhatsApp TV daga yau in muna buƙatar hakan.


1.2. abubuwa na gaba da ya kamata mu sani dangane da WhatsApp TV sune:

WhatsApp TV yana buƙatar status viewers dayawa


WhatsApp TV yana buƙatar tsararren logo


WhatsApp TV yana buƙatar Update akai akai


WhatsApp TV yana buƙatar gudanar da ayyuka kamar na gidan TV wato shirye-shirye na musamman masu nishaɗantarwa da faɗakarwa da kuma ban al'ajabi misali idan muka lura da gidajen TV zamu ga abubuwan da suke yi har yasa mutane suke bibiyar su to wannan ake buƙata kawai gwargwadon yadda mutum zai iya saide banbancin shine a WhatsApp TV ana sanya gajerun abubuwa ne kawai.


1.3. Abunda yasa akafi so ayi amfani da WhatsApp business a TV ɗin;


WhatsApp business yanada features ɗin da normal bashi da su kamar irin su business description Wanda ana buƙatar su a WhatsApp TV, da automatic reply dss.


1.4 Abubuwan da ake buƙata dan buɗe WhatsApp TV:


1. Wayar android mai a ƙalla 4gb Ram da 64 GB Rom SBD dan ana buƙatar ɗaukar nauyin abubuwa dayawa 


Ana buƙatar a sanyawa TV ɗin suna mai ma'ana


Tsara logo mai kyau na WhatsApp TV


Email akan waya da za'a yi saving na phone numbers


Tara phone numbers dayawa akan wayar (yawan lambobin; waya yawan samun kuɗi)


Tsara abubuwan nishaɗi na video


Tsara abubuwan nishaɗi na audio


Tsara abubuwan nishaɗi na photo


Tsara abubuwan nishaɗi na rubutu


Tsara abubuwan ilmantar wa 


Wadataccen lokaci dan aiwatarwa


1.5. Yadda za'a fara WhatsApp TV:


Bayan duk an tanadi komai na abubuwan dana lissafa a sama shikenan sai kuma;


a tsara tsare-tsaren gabatarwa da kuma saƙon neman mutane suyi saving number ɗinku domin su kasance daga cikin masu kallon status na ku misali; "Albadar WhatsApp TV muna buƙatar kuyi saving number ɗinmu dan kallon status ɗinmu masu amfani da koyar da abubuwa" da kuma bibiyar ’yan’uwa da abokai cewa suyi saving number ɗinku Kai tsaye.


Bayan haka kai tsaye za'a fara gwada yawan viewers ta hanyar sanya status guda biyu Yayin da za'a ƙara sanya wasu guda biyu again bayan kowacce awa uku ta hakane za'a ga yawan viewers ɗin ko yakai afara gudanar da WhatsApp TV (a ƙalla ana buƙatar adadin yakai 1k viewers)


Bayan haka dole ne a lura da irin abubuwan da sukafi jan hankalin mutane masu kallon status za'a gane hakan ne kuwa ta hanyar yawan reactions ɗin su akan status, har ila yau dole ne a kula da lokutan sanya status kamar safiya, yammaci dakuma dare sannan a dinga ƙaranta status wato kar a saka dayawa sannan kuma a dinga sanya guda biyu sai bayan awa uku a ƙara sanya guda biyu kada kuma a sanya sama da guda goma a 24 hours


1.6.  Hanyoyin samun kuɗi da WhatsApp TV:


Karɓar tallace tallacen mutane; a matsayin ku na masu WhatsApp TV yawan viewers ɗin ku yawan kuɗaɗen da zaku chaji masu baku tallace tallace kuma zaku tallata cewar kuna karɓar tallan ne a WhatsApp status na ku tare da gamsar da cewa kun kai matsayin WhatsApp TV da adadin viewers sama da dubu ɗaya ta hanyar saka screenshot dan tabbatar wa.


Tallata kasuwancin kanku da irin ayyukan da kuke yi: mutum zai iya amfani da WhatsApp TV ɗin sa kawai in yanaso domin tallata kasuwancin sa ko sana'ar sa ga masu bibiyar sa sama da dubu ɗaya


Affiliation marketing; mutum zai iya yin rijistar affiliation marketing da wasu kamfanoni sannan ya dinga saka link ɗin tare da bayanai ataƙaice na wannan tallan yadda duk wanda ya siya shikuma zai samu commission ɗin sa daga kamfanin


Referral business; wannan ma tsari ne da Mutum zai samu kuɗi a WhatsApp TV ta hanyar tallata duk wasu shafuka da Application masu amfani da suke biyan referral mai kyau wato kuɗi mai tsoka '.


Kar kuji da wai akwai WhatsApp TV sama da dubu uku a Nigeria kuma akwai wanda sun samu miliyoyin nairori da wannan harkar kuma kowa zai iya farawa nan take abunda kawai ake buƙata bayan wanda na faɗa a sama shine jajircewa da sanyawa a rai cewa za'a iya


1.7.. Yadda za ayi growing na audience a WhatsApp TV; growing up na WhatsApp TV ɗin shine abu mafi muhimmanci dan haka dole ne ayi amfani da dabarun da zasu sa a samu mutane masu saving number ɗin WhatsApp TV ɗin dayawa wato ta hanyar tallata hakan a facebook da sauran social media handles, da kuma yawan bayar da lambar WhatsApp kokuma koyar da wasu skills a online ta WhatsApp yadda za'a bayar da lambar ga duk mai buƙata yayi magana kai tsaye sai a buƙaci mutum yayi saving number ɗin kafin ya samu damar shiga wannan ajin na kyauta wato ta hanyar "free skills Training monetisation"


1.8. Kammalawa; WHATSAPP TV a taƙaice na nufin samar da yawan masu kallon status da kuma yawan Update akan abubuwa masu amfani da nishaɗi.


babu shakka duk wanda suka bi wannan hanyar sun dace da kafa WhatsApp TV ɗin su kuma sunyi nasara babban abun buƙatar shine koyon tsarin haɗa video takaitacce da kuma yankewa da editing wato de video editing and organising.

*

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post