YANZU-YANZU: Sanatoti 67 Ne Ke Goyon Bayan Dr. Abdul'aziz Yari, Domin Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Inji Sanata Abdul Ningi
...Abdul Ningi yace dole a bar Sanatoti su zabi son ransu babu wanda ya isa ya kakaba musu wanda basu so
Tsohon mataimakin masu rinjaye a majalisar dattawa ta bakwai, Abdul Ningi ya ce akalla sanatoci 67 ne ke mara wa Abdulaziz Yari baya a neman takarar shugabancin majalisar.
Sanata Ningi ya bayyana haka ne yayin taron ganawa da ‘yan jaridu, ya ce lokaci ya yi da za a bari ‘yan majalisa su zabi shugabanninsu.
Yari wanda yake wakiltar Zamfara ta Yamma kuma tsohon gwamnan jihar ya na daga cikin wadanda suka nuna sha’awar tsayawa takarar kujerar majalisar.
Jam’iyya mai mulki ta APC ta zabi Godswill Akpabio a matsayin wanda zai gaji shugabancin kujerar majalisar, cewar TheCable.
A cewar Ningi: “Lissafinmu na baya-bayan nan, ya nuna cewa a jiya Talata 6 ga watan Mayu, mambobi na kara nuna goyon bayansu.
“Ni ba dan jam’iayyar APC ba ne, ban san yadda kwamitin tsare-tsarensu ya ke ba, amma shekaru 20 kenan ana samun matsala saboda kakaba wa ‘yan majalisa shugabanni tun lokacin Enwerem da Chuba.
“Ya kamata a bari mambobi su zabi wandanda suke so a ra’ayi na, jam’iyyar PDP sun yi kuskure makamancin wannan, ya kamata APC su guji aikata haka, kamar yadda jam’iyyar ta zabi shugabanta haka ya kamata majalisar ma su zabi shugabanninsu.
Ya kara da cewa Abdulaziz Yari yana da kwarewar da ya dace da zama shugaban majalisar.
Sanatan ya kara da cewa: “Tabbas, Yari yana da kwarewar da zai rike shugabancin majalisa, shi yasa muke goyon bayansa, muma mun rike mukamai a majalisar ba wai ‘yan kallo kadai ba ne, ana bukatar irinmu don aiwatar da abin da ake bukata, goyon bayan Yari ba maganan kudi ba ce.”
