Dr. Abdul'aziz Yari yana daya daga cikin muhimman mutane a Afirka mahaddata Al-Qur'ani da kasar Saudiya ta budewa dakin Allah mai tsarki na Ka'aba.
Dr. Abdul'aziz Yari mahaddacin Al-Qur'anine gan-garan kuma masanin ilmin Addinin musulunci dai-dai gwargwado, Dan siyasa ne mai kokarin cika alkawari fiye da sauran 'yan siyasa kuma hamshakin dan kasuwa ne, yana taimakon Addinin musulunci sosai duk kungiyoyin Addinin musulunci na Arewa babu wadda bai taimakawa ba, kuma yana kan taimakon su a kowane lokaci da bukatan hakan ya taso.
A lokacin da Dr. Abdul'aziz Yari yake Gwamnan jihar Zamfara ya yiwa al-ummar manyan ayyuka da Tituna masu dumbin yawa da manyan Gadoji da sauran abubuwan more rayuwa, a bangaren rashin tsaro da jihar take fama dashi ya yaki 'yan bindiga da gaske bai taba yadda da batun sasancin karya da suka dinga yaudarar wasu Gwamnoni ba, har Dr. Abdul'aziz Yari ya kammala Gwamnan jihar Zamfara babu wani kauye ko gari guda daya da 'yan bindiga suke rike dashi ko suke mulki a cikin shi, kullum suna boye a cikin kurmin daji sai dai in su fito sukai hari da an biyo su za'a kashe su sake shigewa daji su boye.
Wallahi wadannan su ne halayensa da na sani kuma na tabbatar da su shekaru 4 da na yi ina aiki tare da shi.
•Yawan karatun Al’Qur’ani.
•Yawan Azumi.
•Rashin wasa da Sallah.
•Girmama mahaifiyarsa.
•Hakuri.
•Kunya.
•Kara.
•Tausayi.
•Taimako.
•Gaskiya.
•Rikon amana.
•Magana daya.
•Juriya.
•Taimakon makiyi.
•Rashin yawan magana.
•Karshen fushinsa ya girgiza kansa.
•Idan ya ji haushin abunda aka yi, sai ya yi tsaki.
•Kawar da Ido.
•Baya jin tsoro.
•Baya rikon abunda ya wuce.
•Baya girgiza saboda makiyi.
•Baya sauraren karamar magana.
•Ba a sukar mutum a gurinsa har sai ya gani da kansa.
•Yana baiwa kowane ma’aikacinsa damarsa.
Bance lallai Dr. Abdul'aziz Yari yafi kowane dan siyasa a Najeriya nagarta ba, amma na tabbata yana gaba-gaba cikin 'yan siyasar da suka fi sauran kokarin kamantawa, bance baya kuskure ba, tabbas kowane dan Adam yana kuskure.
Muna rokon Allah (SWT) ya cigaba da daga kima da mutuncinsa, Allah (SWT) ya kara masa lafiya, arziki da daukaka alfarmar Annabi Muhammad (SAW).
Al'mansoor Gusau
Babban daraktan yada labarai na mai girma tsohon Gwamnan jihar Zamfara Sanata Dr. Abdul'aziz Yari Abubakar.
