Kungiyar musulmai ya duniya tayi taron gaggawa domin daukan mataki saboda a kau cewa sake mai maita sake kuna Qur'ani.
Jami an yan sanda ne suka ba shi kariya kafin ya aiwatar da aniyar tasa, wanda ya ce ya yi hakan ne don ya nuna 'yancinsa na faɗar albarkacin baki.
Dole ne mu ci gaba da tunasar da ƙasashen duniya game da aiwatar da dokokin ƙasa da ƙasa da gaggawa, waɗanda suka haramta nuna duk wata ƙiyayya ga addinai."
Lamarin ya jawo zanga-zanga a faɗin duniya, inda ƙasashen Musulmi kamar Daular Larabawa da Moroko da Kuwait da Iraƙi suka kira jakadan Sweden don nuna ɓacin ransu
Kungiyar Mai mabiya 57 wato Organization of Islamic Countries ( O I C ) ta bawa mabiyan nata shawara da su dauki mataki lokaci daya.
A yau lahadi ne kungiyar ta gana a birnin Jeddah na Saudiyya don lalubo martanin da za su mayar kan ƙona Ƙur'anin da Salwan Momika, ɗan asalin Iraƙi mai shekara 37, ya yi bayan ya tattaka shi a ƙofar wani masallaci a birnin Stockholm.
