Haƙiƙanin zance akan Mining da airdrop..
Na taɓa tambayar wani mai nazarin Hausa a rubuce kan cewar ya za'a fassara kalmar "Mining" da Hausa ya faɗa mun cewa a iya ƙiran shi haƙar ma'adinai na dijital wanda kuma hakan yana nufin za'a iya samu ko a rasa.
Idan ana son ayi bayani mai gamsarwa akan Mining dole ne a fara da previous knowledge/experience wato yadda muka san cewa a irin jihohin zamfara da kebbi da wani ɓangare na Borno da wasu yankunan ƙasar Nijar ana samun tururuwar masu haƙar dinare da wasu ma'adinai masu darajar gaske wanda kuma sun kasu kala biyu wato akwai kamfanoni masu lasisin yin haƙar wanda sun cika ƙa’idar gwamnati kuma suna biyan haraji akwai kuma ’yan neman arziƙi kawai wanda babu wata ƙa’ida da suke cikawa kuma suna yin haƙar ne ta gargajiya kawai.
Idan mun fahimci wannan to laa shakka zamu iya fahimtar Mining da ake yi na Crypto abu nafarko shine cewar babu fa tabbas akan kowane irin Coins ɗin da ake Mining amma kuma ba'a san me gobe zatayi ba bitcoin na daga cikin Mining ɗin da akayi nasara akan su a duniya kuma wanda basuyi ba sunyi dana sani Banbancin dake tsakanin Mining da ake yi na haƙar ma'adinai da wannan nan na Crypto shine traditional Mining yafi wahala matuƙa amma shi kuma yafi Zama safe ga wanda suke yin sa Eh! Ina nufin hakan domin kuwa akwai mining dayawa da akeyi wanda kuma ba na gaskiya bane kawai wani salo ne na ta tsar bayanan mu kokuma siyarwa da wasu kamfanoni bayanan mu kokuma kawai dabara ce ta tara community domin ayi monetisation ɗinsu ta hanyar ɗaura tallace tallace wajibi ne muyi ta-ka tsan-tsan sosai domin kula da Abunda zamuke shiga.
Ana samun kuɗi da Mining sosai bayan bitcoin anyi su dayawa kala kala wasu sun tafi a banza sun lalace wasu kuma sun yi nasara an samu kuɗi da su wanda akayi kwanan nan sune irin su core da renec da kuma PI da akayi ta cece-kuce daban daban akan sa. Amma babu wani tabbacin Mining sai de in har yayi nasara an gani.
Airdrop kuwa galibin su wata dabara ce kawai ta tara mabiya da kuma sanya abunda ake cewa community ads wato kowa ya zama yana tallata wannan coin ɗin.
Airdrop kawai na nufin cewa a ƙirƙiri wani coin da bashi da liquidity ma'ana babu wani dalili da zai sa ya zama kuɗi ko a siye shi da kuɗi sai ace duk wanda yayi rijista za'a bashi adadi mai yawa wanda kuma dazaran anyi launching zai fito da daraja wannan dalilin yasa mutane suke yaɗa wa tare da tallatawa har coin ɗin ya samu irin community ɗin da yakeso kafin ya iya yin nasara ko akasin haka
Bai kamata mu dinga yin buri ba dan muna Mining ko mun shiga wani airdrop sannan bai kamata mu gusar da hankalin mu ba akan Mining ko airdrop yadda kowane Mining in yazo sai munyi Ruu mun shiga batare da la’akari da cewa mai inganci ne ko mara inganci ba yanada kyau muke bincike abu dai dai gwargwadon ilimin mu dan kar mu zana ’yan amshin shata.
Mining gaskiya ne hakama airdrop gaskiya ne amma fa mu sani cewa dukkanin wani abu na gaskiya anayin na ƙaryar sa dan acuci wasu.
Asalin mining da Manyan injina akeyin sa shiyasa duk da yajima anayin sa mu bamu san shi ba Kusan saida aka fara yin sa a computer da wayoyin hannu.
