Artificial intelligence da barazanar rasa sana'o'in bil adama..


 Artificial intelligence da barazanar rasa sana'o'in bil adama..


Har yanzu ban sauya akan fahimta ta ba cewa tsarin artificial intelligence baze sa ’yan adam su rasa sana'o'in su ba sai de ma yaƙara yawan aikin a duniya da kuma sauƙaƙa hanyoyin samun kuɗi.


Bayan ikirarin shahararren kamfanin "Stability AI" ma mallakin manhajar "Stable diffusion" tattaunawa ta kaure a tsakanin matasan da ke hanƙoron gina kasuwanci a doron Technology wato Tech. Industry a wani yunƙurin wata ƙungiya da ake ƙira Nigerian Young entrepreneurs(Digital entrepreneurship) an yi musayar fahimta wanda ina daga cikin wanda suka bayyana fahimtar su duk da cewa ni fahimtar da nake da ita a bayyane take na sha faɗa a irin wannan yanayin.


Abunda ake nufi gwari-gwari shine cewar ayyukan programming da ayyukan graphic design da video editing duka Fasahar AI zata ƙwace to ina madogarar ɗaliban dake karatun programming da software development yanzu? Wannan ita ce tattaunawar da ta sake zama sabuwa bayan da kamfanin Stable AI yayi iƙirari cewa nan da shekara biyar za'a nemi ɗan adam mai yin programming a rasa kun san da me kamfanin ya dogara?


Ya dogara ne da wata ƙa’idar psychological entrepreneurial ethics cewar duk Abunda yazo da sauƙi kuma yafi kyau to babu shakka zai samu karɓuwa kuma hakane domin fasahar AI tana sauƙaƙa abubuwa misali idan zaka biya 5k ayi maka logo na ɗan Adam to a AI kuma subscription kawai zakayi na sati ɗaya da wannan 5k ɗin kuma AI sai yayi sati yana maka design kala kala sannan kuma yanzu kamfanonin kala kala ne akwai wanda fasahar AI ɗinsu tafi ta mutane nuna kyau da ƙwarewa da kuma yin aiki da sauri wannan duk suna daga cikin abubuwa masu muhimmanci da kamfanin Stable AI ya kalla yayi wannan ikirarin na shi.


Mecece fahimta ta akan hakan?


Har yanzu ina kan fahimtar cewa fasahar AI bazata rage ayyukan yi a Tech industry ba sai de zata riɓanya ayyukan ne fiye da yadda ake tunani a kwanakin baya wani kamfanin ƙirƙira a Japan ya bayyana wuraren kamawa a dogara da su a ɓangaren a matsayin wani abu da har duniya ta tashi baza’a iya cike guraben ba na yadda 100%100 da wannan fahimtar ganin cewa AI yana ƙwace aikin mutum dubu ne sannan yazo da sababbin ayyukan Mutum miliyan dubu bani na fara faɗa ba wani David innoson ne ɗan asalin ƙasar Faransa yafara faɗa.


a yadda nake fahimta shine yanzu lokaci ne na dogaro da Kai kai tsaye wato financial freedom ga kowane mutum da ya shigo harkar Tech industry kuma na gamsu da cewar AI zai cigaba da taka rawar gani a rayuwar mu da kuma zuwa da sauye sauye kuma dukkan dalilai na karɓar shi sun bayyana.


Amma ta yaya AI zai ruɓanya ayyukan yi mai makon ragewa?


Amsar farko itace AI ɗin yanayin kan sa ne?

Eh za'a iya cewa hakan kamar yadda ɗan Adam yake haihuwar ɗan adam haka shima AI zai iya programming ɗin ɗan’uwan sa AI amma fa da idea ɗin ɗan adam shine zai tsara komai, babban misalin da nake bayarwa shine yadda dubban mutane suka rasa aikin su a wasu kamfanonin sadarwa daga ɓangaren sarrafa Data da airtime yayinda aka rasa dubban guraben aikin a ɓangare ɗaya kuma sai aka samu ɓangarorin dogaro da Kai na ƙashin kai sama da miliyoyin mutane sun zama CEO (s) mai makon ordinary workers sun samu yan ci a sana'ar su ma'ana bayan sallamar ma'aikata dubbai Dalilin da yasa aka sallame su kuma shine dalilin da ya haifar da miliyoyin mutane suka mallaki kamfanonin siyar da data ta hanyar VTU website da ba'a kori ma'aikatan ba da ba'a samu damar ba kamar yadda da ba'a samu ɓullar AI ba da ba'a samu wasu damar makin ba.


Nan gaba kaɗan samun kuɗaɗe a duniya zai ƙaru da kaso mai yawa sai de amfani da kuɗin ma zai ƙaru SBD babu abunda zai zama na kyauta a nan gaba kusan komai sai ya zama na biyan kuɗi dan haka kuɗaɗen zasu rage daraja.

*

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post